ABNA24 : Rear Admiral Hossain Khanzadi ya ci gaba da cewa; Atisayen da sojojin manyan kasashen uku, Iran, China da Rasha za su yi, sako ne ga duniya akan cewa suna da karfin da za su kawo sauyi a fagen siyasar duniya.
Har ila yau kwamandan sojan ruwan na Iran ya yi ishara da rawar dajin da sojojin kasar su ka yi, mai taken Zulfiqar 99, da yadda kafafen watsa labara na waje su ke dauke ta.
Haka nan kuma ya ambaci yadda wasu jiragen Amurka biyu marasa matuki su ka yi kutse a sararin samaniyar Iran da yadda, amma makaman da Iran din ta kera su ka taka musu birki da tilasta musu ficewa.
342/